Posts

Al'ummar Jahar Katsina Musamman Wadanda Ke Rayuwa A Yankunan da Aka Yi Sasanci Tsakaninsu da Yan Ta'adda Na Ci Gaba da Tofa Albarkacin Bakinsu Game Da Lamarin

Image
SU WAYE 'YAN TA'ADDA, KUMA ME SUKE SO BUKATA? 'Yan ta'adda gungun wasu mutane ne da suka bijire wa doka, kuma suka mallaki makamai ta haramtaciyyar hanya domin biya wa kansu bukatu ta hanyar amfani da makami. Sukan yi amfani da makami su kwaci dukiya, sannan su yi garkuwa da mutane domin amsar kudin fansa. A wajensu, illata lafiyar al'umma ba komai ba ne. Haka kuma, sukan kashe rayukan al'umma duk domin su biya wa kansu bukatu. MENE NE BUKATARSU? Sau da dama sukan isar da sako musamman ta hanyar wadanda suka kama don yin garkuwa da su a kan cewar suna da bukatu da yawa da suke so Gwamnati ta biya masu. Lokaci da yawa sukan bayyana cewa a yi masu adalci. A ba su ilimi, a kula da lafiyarsu, a yanka masu labi (Wajen kiwon dabbobi) da dai sauransu. Wasu kuma ba ruwansu da wadannan bukatun, kullum abinda suke nuna wa jama'a shi ne, jihadi suke. A INA SUKE RAYUWA? Kamar yadda al'ummar da abin ya shafa suka bayyana, mafi yawan al'ummar da ake s...

Martanin Óusmañe Dembele Zuwa Ga Magoya Bayan Kungiyar Barcelona.

Image
"Sun ce ta kare man. Sun man dariya lokacin da na fadi. Suna kira na mai rauni, mai rauni, gwanin banza. Abin da ba su gani ba shi ne daren da nake tashi in yi kuka ni kadai. Zuciyata kan yi zafi sosai. Wani lokaci sai in ji kamar in daina taka leda. Ba su taɓa ganin sa'o'in farfadowata ba. Kadaici da shakku, tabbas sun yi ƙoƙarin karya ni, amma sai na dage. Don haka wannan "Ballon d’Or" ba ganima ce kawai ba—alama ce ta tsira. Duk tabo, duk wani koma-baya, duk daren rashin barci ya kawo ni nan. Wannan kyauta ta zinari tana haskakawa, amma tafiyata zuwa gare ta an gina ta cikin duhu. Ga waɗanda suka gaskata ni lokacin da duniya ta juya man baya, wannan naku ne. Kuma ga waɗanda suka yi shakka… na gode, kun ƙara ƙarfafa ni. 🖤🏆"

Wani Magoyi Bayan Kungiyar Barcelona Ya Yi Allah-wadai Da Kungiyar FIFA.

Image
Biyo bayan nasarar da Dembele ya samu, wani magoyi bayan Barcelona ya yi tur da wannan nasara ta Óusmañe Dembele. A cewarsa, ya bayyana cewa sam wannan kyauta ba ta dace da Dembele ba. 

A can baya 'yan kungiyar Barcelona sun taka wasa sosai da Óusmañ Dembele. Bayan ya bar kungiyar kuma, sai suka kasance suna yi masa mummunar fata sakamakon rabuwar baram-baram da suka yi da shi. A cewar wasu magoya bayan Barcelona din, Dembele bai iya taka leda sosai ba. Cikin iyawar Allah, yau sai ga shi Óusmañ Dembele ya lashe kyautar gwarzon dan wasan da ya fi kowa iya taka leda a shekarar 2024. Ya kuma samu wannan nasarar ne bayan komawarsa kungiyar "Paris Saint German". Ke nan dai za a iya cewa, Allah Ya nufi dan wasan da samun sa'ar rayuwa a Kwallon kafa.

Image

Kowa da bikin zuciyarsa

 Ni a ra'ayina, kallon kwallo bai dace da Bahaushe ba.