Al'ummar Jahar Katsina Musamman Wadanda Ke Rayuwa A Yankunan da Aka Yi Sasanci Tsakaninsu da Yan Ta'adda Na Ci Gaba da Tofa Albarkacin Bakinsu Game Da Lamarin
SU WAYE 'YAN TA'ADDA, KUMA ME SUKE SO BUKATA? 'Yan ta'adda gungun wasu mutane ne da suka bijire wa doka, kuma suka mallaki makamai ta haramtaciyyar hanya domin biya wa kansu bukatu ta hanyar amfani da makami. Sukan yi amfani da makami su kwaci dukiya, sannan su yi garkuwa da mutane domin amsar kudin fansa. A wajensu, illata lafiyar al'umma ba komai ba ne. Haka kuma, sukan kashe rayukan al'umma duk domin su biya wa kansu bukatu. MENE NE BUKATARSU? Sau da dama sukan isar da sako musamman ta hanyar wadanda suka kama don yin garkuwa da su a kan cewar suna da bukatu da yawa da suke so Gwamnati ta biya masu. Lokaci da yawa sukan bayyana cewa a yi masu adalci. A ba su ilimi, a kula da lafiyarsu, a yanka masu labi (Wajen kiwon dabbobi) da dai sauransu. Wasu kuma ba ruwansu da wadannan bukatun, kullum abinda suke nuna wa jama'a shi ne, jihadi suke. A INA SUKE RAYUWA? Kamar yadda al'ummar da abin ya shafa suka bayyana, mafi yawan al'ummar da ake s...
Comments
Post a Comment