Al'ummar Jahar Katsina Musamman Wadanda Ke Rayuwa A Yankunan da Aka Yi Sasanci Tsakaninsu da Yan Ta'adda Na Ci Gaba da Tofa Albarkacin Bakinsu Game Da Lamarin

SU WAYE 'YAN TA'ADDA, KUMA ME SUKE SO BUKATA?

'Yan ta'adda gungun wasu mutane ne da suka bijire wa doka, kuma suka mallaki makamai ta haramtaciyyar hanya domin biya wa kansu bukatu ta hanyar amfani da makami. Sukan yi amfani da makami su kwaci dukiya, sannan su yi garkuwa da mutane domin amsar kudin fansa. A wajensu, illata lafiyar al'umma ba komai ba ne. Haka kuma, sukan kashe rayukan al'umma duk domin su biya wa kansu bukatu.

MENE NE BUKATARSU?

Sau da dama sukan isar da sako musamman ta hanyar wadanda suka kama don yin garkuwa da su a kan cewar suna da bukatu da yawa da suke so Gwamnati ta biya masu. Lokaci da yawa sukan bayyana cewa a yi masu adalci. A ba su ilimi, a kula da lafiyarsu, a yanka masu labi (Wajen kiwon dabbobi) da dai sauransu. Wasu kuma ba ruwansu da wadannan bukatun, kullum abinda suke nuna wa jama'a shi ne, jihadi suke.

A INA SUKE RAYUWA?

Kamar yadda al'ummar da abin ya shafa suka bayyana, mafi yawan al'ummar da ake samu da aikata laifin ta'addanci kabilar Fulani ne, musamman a nan Arewacin Nigeria. Sai dai a kan samu tsiraru wadanda ba Fulani ba. Ke nan ana iya samun kowace irin kabila a cikin 'yan ta'adda. Game da wajen zamansu kuwa, mafi yawa suna rayuwa ne a cikin jeji. Sai dai akan samu kadan daga cikinsu da ke rayuwa a cikin birane da kananan garuruwawa musamman na Hausawa.

CE-CE-KU-CEN AL'UMMA GAME DA SULHU TSAKANIN 'YAN TA'ADDA DA  MUTANEN WANI YANKI NA JAHAR KATSINA.

Muhawara mai zafi ta kaure a tsakanin al'umma musamman a kafafen sada zumunta biyo bayan sulhu da wasu yankuna na jahar Katsina suka gabatar da 'yan ta'adda. Yayin da wasu ke bayyana alfanun abun, wasu kuma ke kallon sa a matsayin aikin banza. Wasu na ganin cewa sulhu da 'yan ta'adda abu ne mai hatsarin gaske musamman ganin yadda aka bar su da makamansu a hannu. Lamarin da ya jawo wasu ke kwatanta sasancin da karin maganar Hausawa da ke cewa "an kashe maciji ba a sare kai ba". Wasu kau gani suke sulhun alkairi ne, saboda a dalilinsa suke zuwa gona, su je kauyaku sannan su yi dare a kan hanya ba tare da tsoro ko shakkar 'yan ta'adda za su afka masu ba. A takaice dai har yanzu a kan wannan muhawara al'umma suke.

TSOKACI
Tabbas sulhu alkairi ne a duk lokacin da aka samu sabani, sai dai yana da kyau a yi shi bisa tsari. Jahar Katsina ta yi sulhu da 'yan ta'adda, amma jahar Zamfara ba ta yi ba. Ke nan cikin sauki 'yan ta'addar za su iya shiga Zamfara su yi ta'addanci, sannan  su dawo Katsina su zauna lafiya. Ke nan wannan ba mafita ba ce mai dorewa. Zai fi kyau idan za a yi maganin matsala, a yi ta gaba daya. Bai kyautu a ware wani yanki kadai ba.

Comments

Popular posts from this blog

Martanin Óusmañe Dembele Zuwa Ga Magoya Bayan Kungiyar Barcelona.

A can baya 'yan kungiyar Barcelona sun taka wasa sosai da Óusmañ Dembele. Bayan ya bar kungiyar kuma, sai suka kasance suna yi masa mummunar fata sakamakon rabuwar baram-baram da suka yi da shi. A cewar wasu magoya bayan Barcelona din, Dembele bai iya taka leda sosai ba. Cikin iyawar Allah, yau sai ga shi Óusmañ Dembele ya lashe kyautar gwarzon dan wasan da ya fi kowa iya taka leda a shekarar 2024. Ya kuma samu wannan nasarar ne bayan komawarsa kungiyar "Paris Saint German". Ke nan dai za a iya cewa, Allah Ya nufi dan wasan da samun sa'ar rayuwa a Kwallon kafa.