Martanin Óusmañe Dembele Zuwa Ga Magoya Bayan Kungiyar Barcelona.
"Sun ce ta kare man. Sun man dariya lokacin da na fadi. Suna kira na mai rauni, mai rauni, gwanin banza. Abin da ba su gani ba shi ne daren da nake tashi in yi kuka ni kadai. Zuciyata kan yi zafi sosai. Wani lokaci sai in ji kamar in daina taka leda. Ba su taɓa ganin sa'o'in farfadowata ba. Kadaici da shakku, tabbas sun yi ƙoƙarin karya ni, amma sai na dage. Don haka wannan "Ballon d’Or" ba ganima ce kawai ba—alama ce ta tsira. Duk tabo, duk wani koma-baya, duk daren rashin barci ya kawo ni nan. Wannan kyauta ta zinari tana haskakawa, amma tafiyata zuwa gare ta an gina ta cikin duhu. Ga waɗanda suka gaskata ni lokacin da duniya ta juya man baya, wannan naku ne. Kuma ga waɗanda suka yi shakka… na gode, kun ƙara ƙarfafa ni. 🖤🏆"
Comments
Post a Comment